Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, rahotanni daga majiyoyin hukuma da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a yankin zirin Gaza na nuni da cewa sama da kashi 35 cikin 100 na wadanda hare-haren gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya shafa yara ne da mata da iyaye mata.
Haka nan kuma wasu 'yan jarida biyu na Palasdinawa sun yi shahada a wani harin da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai a safiyar yau 10 watan Oktoba a wani ginin da ake kira Hajji da ke yammacin birnin Gaza.
Shahidai Saeed al-Tawil da Hisham al-Nawajah 'yan jarida ne na falasdinawa da suka yi shahada a harin da yahudawan sahyuniya suka kai kan ginin 'yan jarida a yammacin birnin Gaza.
A cikin shirin za ku ga bidiyon sabon rahoton shahidi Saeed al-Tawil, wanda ke ba da labarin yadda aka kwashe tsawon daren jiya a yankin Hajji.
Mohammad Sobh shi ne dan jarida na uku da ya samu munanan raunuka a wannan harin.
Da gangan gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai hari kan ginin ‘yan jarida a Gaza domin hana su yada abubuwan da suka faru da laifukan da wannan gwamnati ke aikatawa a wannan birni.
Har ila yau, ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a zirin Gaza ta sanar a ranar Talata cewa, yara da mata 208 ne suka yi shahada a zirin Gaza tun farkon yakin guguwar Al-Aqsa. Daga cikin wadannan yara 143 da mata da iyayen Palasdinawa 105 na daga cikin wadanda suka yi shahada a Zirin Gaza.
Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a zirin Gaza ta sanar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a cikin 'yan kwanakin da suka gabata ya kai mutane 704.
A cewar rahoton na wannan ma'aikatar, adadin wadanda suka jikkata ya kai kimanin mutane dubu hudu.